Tallafi

Yadda Zaka Cike Sabon Program Na NITDA Na Ninja Accelerator

Yadda zaka cika sabon tallafin NITDA mai suna Ninja accelerator program.

Shidai wannan program din mai suna Ninja accelerator program shirine da Japan international cooperative agency wato JICA da kuma hadin gwuiwa da national information technology development agency wato NITDA suka hada kai dan samar dashi

Saboda su daga masu kasuwanci wato entrepreneur don cigaban kasuwancinsu da suke gabatarwa

Sannan bangarori uku ne kawai zasu iya shiga cikin wannan kasuwanci

1. Agriculture:- wato masu harkar noma bawai sai na shukaba a a harda kiwo

2. Health:- masu harkar lafiya asibitoci da dai sauransu

3. Cleantech:- Su kadaine mutum zai iya cikawa

 

Yadda zaka cika shine kashiga https://ninjaaccelerator.ng/ idan ka shiga saika yi kasa ka karanta yadda program din yake sannan inka gama saika danna kan Apply now
idan ka danna zai kaika kan google form ne inda zaka cika wannan abun

Dan haka saika cike komai a natse kayi submit.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button