KIMIYAR NA'URA

Yadda Ake Kira Kyauta Kuma Batare da Layiba da WIFI Network

 A koda yaushe abinda mutane ke bukata shine, samun wata hanya wadda zata rage musu kashe kudi musammam ma a wannan lokaci na COVID 19 da abubuwa suke ta kara tsada, wannan daliline yasa muka nemo muku wannan yanyar na yadda zaka iya kiran waya kyauta ta hanyar amfani da WIFI network.

Free Call

  Za’a ya amfani da WIFI Local Area Network gurin sadarwa tsakanin  na’ura da na’ura ko waya zuwa waya  wanda bazai gaza sama da meta 50 ba, sabida WIFI network baya da nisan taza kamar cellular Network wanda ke amfani da SIM Card.

 Wannan Shi yasa ake amfani da WIFI network gurin sadarwa a rukunin ma’aikatu da ofisoshi, ta yadda za’su dinga sadarwa kansu bayani stakanin Ofishi da Ofishi da ke cikin da’irar ma’aikata daya, Kamar Bankuna, Police Station  da sauransu.

 Batare da bata locaki ba zan kaiku ga yadda zaka iya kiran waya kyaufa tsakanin waya da waya ko rukunin wayoyi  wadanda basu gaza sama meta  50 da WIFI Network.

Fasali na Kira da Wifi Network 

  • Baya bukatar Layin waya 
  • Za’a iya jona wayoyi da waya kamar Walkie Talkie 
  • Za’a iya nemo masana sukara nisan tazara na network din 
  • da sauransu

Yadda Ake Kira Kyauta ba Tare da Liyiba da Wifi Network 

a kwai manhajoji da yawa wadanda suke wannan aiki, amma a wannan karo zamuyi amfa da wata manhaja mai suna “WIFI Calling and Walkie Talkie”. Sauke Manhajar (Download Here) 

Mataki 1:- Yi Installin din Manhajar WIFI Calling 

Mataki 2:- Bude Manhajar, Akwai fasahu guda 2 a cikin manhajar, ko dai za ku iya zaɓar WiFi Calling ko Walkie Talkie,

Idan WiFi Call: Waya ɗaya zata danna “+ Call” sannan wata wayar ta jira don karɓar wannan kiran sannan kuma zaku iya magana da juna.

Idan kuma  Walkie Talkie ka zaba: Waya daya ce zata danna “Create Group” wasu kuma har zuwa wayoyi 3 saika danna”Join Group”, sai ka zabi na’urar ka jira har sai an gama kirgawa sannan zaka fara amfani da wannan app din (har zuwa sama da Mita 50).

Duka duka wannan Shine Idan kana da tambaya zaka iya tambayarka a akwatin comment da ke nan kasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button